Matatar Dangote ta karyata ikirarin da kungiyar dillalan man fetur suka yi cewa matatar zata sanya farashin lita kan Naira dari shida.
Sanarwar babban jami’in kula da zuba jari da sadarwa na rukunin kamfanin, Anthony Chiejina, ta karyata ikirarin.
Sanarwar ta ce, kungiyar dillalan man ba abokiyar kasuwancin kamfanin Dangote ba ce a halin yanzu, kuma ba ta tattauna farashin litar mai tare da ita ba, ballantana basu damar izni ko ikon yin magana a madadinsa ba.
Matatar ta bukaci jama’a su yi watsi da Sanarwar, inda ta jaddada cewa, za a sanar da duk wani bayanin farashin a hukumance.