Saurari premier Radio
22.1 C
Kano
Tuesday, September 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar wakilan kasar nan ta musanta zargin da ke cewa kowane ɗan...

Majalisar wakilan kasar nan ta musanta zargin da ke cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya domin rage musu radadin janye tallafain mai.

Date:

Majalisar wakilan kasar nan ta musanta zargin da ke cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya domin rage musu radadin janye tallafain mai.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar ya bayyana iƙirarin – da mataimakin sakataren gamayyar ƙungiyar ƙwadogon ƙasar NLC, Christopher Onyeka ya yi a matsayin zargi mara tushe.
Sanarwar ta Mista Rotimi, ta kuma buƙaci mataimakin sakataren NLC da ya fito ya nemi afuwar majalisar a bainar jama’a.
Mista Rotimi, ya ƙara da cewa akwai bukatar NLC da duk ‘yan Najeriya sun sani cewa a cikin ƙasa da kwana 100 da ƙaddamar da majalisar su, ta yi ƙoƙari wajen inganta jin daɗi da walwalar ma’aikata.
Sakataren na NLC Christopher Onyeka dai ya yi zargin cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya a matsayin tallafin rage raɗaɗi.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...