Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da karatu na biyu kan ƙudirin dokar da ke neman hukunta asibitoci da ma’aikatan lafiya da ke ƙin karɓar marasa lafiya masu buƙatar kulawar gaggawa.
Ƙudirin da Sanata Abdulaziz Yar’Adua ya gabatar ya tanadi tarar naira 300,000 ko ɗaurin watanni shida a gidan yari, ko kuma duka biyun, ga waɗanda suka karya dokar idan aka amince da ita.
Haka kuma, ƙudirin ya buƙaci asibitocin gwamnati da masu zaman kansu su fara tantance marasa lafiya cikin mintuna 15 da zuwansu, tare da fara ba su kulawar farko cikin mintuna 30.
Majalisar ta miƙa ƙudirin ga kwamitinta da ya dace domin ƙarin nazari.
Sai dai ƙudirin bai zama doka ba tukuna, domin akwai sauran matakan da zai bi kafin a amince da shi.
