
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar tabbatar da adalci da daidaito SERAP ta bai wa Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, Farfesa Joash Amupitan, wa’adin kwanaki bakwai domin ya bayyana rahotannin fasaha da binciken tsaro kan na’urorin da hukumar ke shirin amfani da su a babban zaɓen 2027.
Wa’adin ya biyo bayan gwajin amfani da na’urorin tantance masu zaɓe da loda sakamakon zaɓe da INEC ta gudanar a zaben gwaji a ranar 28 ga Nuwamba, 2026, a rumfunan zaɓe 17,676.
Serap ta ce ya kamata hukumar ta bayyana sakamakon gwajin, matsalolin fasaha da aka gano, matakan gyara da aka ɗauka, da kuma adadin masu zaɓen da suka halarta da waɗanda aka tantance.
Ta kuma buƙaci INEC ta bayyana rahotannin binciken tsaro mai zaman kansa, gwajin kutsen kwamfuta da sauran tantancewar da aka yi kan na’urar BVAS da tsarin tattara sakamakon zaɓe na IReV.
Haka kuma, ta nemi hukumar ta bayyana irin raunin da aka gano a waɗannan na’urori da matakan da aka ɗauka domin hana kutse, sauya bayanai ko yin maguɗi.
Serap ta ce ‘yan Najeriya na da haƙƙin sanin ko fasahar zaɓen da INEC za ta yi amfani da ita tana da inganci, tsaro kuma za a iya tantance sahihancinta ba tare da dogaro da bayanan hukumar kaɗai ba.
Ta kuma ƙara da cewa bayyana waɗannan bayanai da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a da sahihancin zaɓen 2027.
