Mataimakin gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da shawarwari masu amfani daga masu ruwa da tsaki da sauran masu fatan alheri domin bunkasa ci gaban jihar.
Murtala Sule Garo ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin tsohon dan takarar Gwamnan Kano Alhaji Kabiru Inuwa Waya a ofishinsa.
Mataimakin gwamnan ya yaba da irin gudunmawar da Waya yake bayarwa wajen ci gaban siyasa da al’umma, inda ya cc gwamnati za ta ci gaba da hada hannu da duk masu kishin cigaban Kano.
Tun da farko, Alhaji Kabiru Inuwa Waya ya ce ziyarar tasa na da nufin taya Mataimakin gwamnan murna ne, tare da yin alkawarin ci gaba da bawa gwamnatin Kano goyon baya a kowane mataki da fanni.
A nasa bangaren, dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar karamar hukumar Birni, Nabil Sarki Aliyu Daneji, ya bayyana Kabiru Inuwa Waya a matsayin daya daga cikin masu cikakken goyon bayan gwamnatin jihar Kano.
