Jihar Kano ta koma matsayi na uku cikin jihohi 36 na Najeriya a kididdigar ingancin tsarin kula da sauyin yanayi na shekarar 2026, bayan samun gagarumin ci gaba cikin shekaru biyu.
Kididdigar ta nuna cewa Kano ta tashi daga matsayi na 35 a shekarar 2024 zuwa na hudu a 2025, kafin ta koma matsayi na uku a wannan shekarar.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Kano, Dr Dahiru Muhammad Hashim, ya dangant ci gaban da sauye-sauye da tsare-tsare da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bullo da su domin inganta kula da sauyin yanayi.
Dr Dahiru ya ce daga cikin matakan da kano ke dauka akwai shirin dasa itatuwa miliyan 10, wanda ya biyo bayan raba itatuwa sama da miliyan 5 da dubu 500 a kananan hukumomi 44 a shekarar 2025, tare da amfani da fasahar zamani wajen bibiyar wuraren da aka dasa su da kuma tabbatar da sun rayu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na cewa Kano za ta kara karfafa matakan yaki da illolin sauyin yanayi, musamman ambaliya, zaizayar kasa, karancin ruwa da gurbatar muhalli, tare da neman tallafin kudi da karfafa hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kan su domin tabbatar da dorewar ayyukan.
