Saurari premier Radio
24 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwankwaso ya bayyana takaicin yadda aka tsalleke gwamna Abba Gida-Gida cikin gwamnonin...

Kwankwaso ya bayyana takaicin yadda aka tsalleke gwamna Abba Gida-Gida cikin gwamnonin da aka rabawa tallafin shinkafa

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayyana takaicin sa kan yadda aka tsalleke gwamnatin Kano cikin gwamnonin jihohi 35 da aka rabawa tallafin shinkafa.

Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana hakane a shafukan sa na sada zumunta a ranar Litinin.

Kwankwaso, ya ce an mika kason Kano hannun APC maimakon yadda aka baiwa kowane gwamna.

Ya ce wannan cin fuska ne ga kundin tsarin mulki na Dimukuradiya da nuna bangaranci na jam’iya.

Yayi kira ga shugaban kasa Tinubu da ya gaggauta dakatar da wannan dambarwa dake neman tintsirar da Dimukuradiya.

Sanata Kwankwaso ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda aka sauya daraktocin DSS uku a Kano cikin makonni 2.

Ya ce wannan sauye sauye na shafar tsaron jihar Kano.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...