Kungiyar tuntuba ta Arewacin kasar nan, ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen fara aikin horas da mutane sana’oi, tare da basu jari a nan Kano.
Shugaban kungiyar reshen jiha, Dr. Umar Faruk Umar da ya bayyana haka lokacin kaddamar da bude sabon ofishinta a nan Kano, ya ce za su dauko wadanda za a ba jarin daga gidajen da suka chanchanta, tare da tabbatar da ganin ana sa ido domin gudanar da sana’oinsu.