Saurari premier Radio
29 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKungiyar Likitoci ta kasa, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki idan har...

Kungiyar Likitoci ta kasa, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki idan har ba a sako abokiyar aikinsu ba.

Date:

Kungiyar Likitoci ta kasa, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki idan har ba a sako abokiyar aikinsu, Dokta Popoola Ganiyat kafin ranar 26 ga watan Agusta ba, da aka yi garkuwa da ita.

Shugaban kungiyar, Dr. Dele Abdullahi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai jiya a Abuja.

Dr. Abdullahi ya ce, kungiyar ta daina hakuri da halin ko-in-kula da gwamnati ke nunawa kan sace Dr. Ganiyat.

An dai yi garkuwa da Dr. Ganiyat, wacce ma’aikaciya ce a sashin kula da lafiyar ido da ke cibiyar kula da ido ta kasa, Kaduna, a ranar 27 ga watan Disamba, 2023, tare da mijinta da kuma dan yar uwarta.

An saki mijinta a watan Maris, amma Dr. Ganiyat da danta suna tsare a wurin masu garkuwar.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...