Saurari premier Radio
25.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar Kano Patriotic Front ta kaddamar da dashen bishiya dubu dari biyar...

Kungiyar Kano Patriotic Front ta kaddamar da dashen bishiya dubu dari biyar a fadin jihar

Date:

Kungiyar kishin Kano ta Kano Patriotic Front ta kaddamar da dashen bishiya dubu dari biyar a fadin jihar.

Wannan wani bangare ne na magance matsalar dumamar yanayi da zaizayar kasa da majalisar dinkin duniya da suran masu ruwa da tsaki a fannin yanayi da muhalli suka jima suna kokarin dakilewa.

Da yake zantawa da Premier Radio yayin kaddamar da dashen bishiyun, shugaban kungiyar, Major Janar Ibrahim Sani mai ritaya, ya ce sarewa da kona itatuwa da ya zama ruwan dare yana matukar barazan ga lafiyar al’umma.

Ya kara da cewa kungiyarsu ta kudiri aniyar dashen bishiya dubu dari biyar a fadin jihar Kano.

Wakilinmu Shehu Usman Salihu ya rawaito cewa, taron da aka gudanar a dakin taro na Fagge Islamic Centre dake Tudun Bojuwa, ya samu halartar masu ruwa da tsaki dake aiki kan magance matsalar dumamar yanayi a jihar Kano.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...