Ƙungiyar Enhancing Financial Innovation & Access, EFINA, ta fitar da sakamakon binciken Access to Financial Services in Nigeria, A2F 2026, wanda ya nuna cewa kashi 61 cikin 100 na matasa a Najeriya na fama da talauci.
Binciken ya duba yanayin harkokin kuɗi da damar da matasa ke da ita wajen amfani da ayyukan kuɗi, inda ya nuna cewa mafi yawan waɗanda ke fama da talaucin na fuskantar ƙalubale wajen biyan bukatun yau da kullum da kuma tafiyar da kuɗaɗensu.
EFINA ta ce sakamakon binciken na da muhimmanci wajen fahimtar matsalolin kuɗi da al’umma ke fuskanta, da kuma samar da hanyoyin inganta damar samun ayyukan kuɗi da ƙarfafa tattalin arziki.
