Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani gawurtaccen dan daba da ya addabi unguwar Dorayi mai suna Auwalu Ali wanda aka fi sani da Auwalu Dan Daba.
wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Litinin 2 ga Fabrairu 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa an cafke Auwalu Ali mai shekaru 26, wanda aka fi sani da Auwalu Dan Daba, bayan samun sahihin bayanan sirri da ke nuna cewa yana hada tawagar ƴan daba domin kai hare-hare da sace-sace ga jama’ar Dorayi.
Sanarwar ta kara da cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bukaci al’umma su riƙa kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa domin ɗaukar matakin da ya dace.
