Matakin ya biyo bayan wani bincike na farko da hukumar NCAA ta gudanar, inda ta gano cewa kamfanin jirgin ya aika wa fasinjojin sanarwar da ba daidai ba game da tashin jirgin.
Rahoton ya ce wani lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Inibehe Effiong, ya soki Air Peace kan abinda ya bayyana a matsayin rashin kulawa da fasinjoji, bayan jirginsa daga Legas zuwa Enugu ya samu jinkiri har zuwa yamma.
NCAA ta buƙaci Air Peace ya gabatar da tsarin diyya ga fasinjojin da abin ya shafa, bayan tantance matsalar da kuma yadda aka sanar da su game da jinkirin jirgin.
