Babbar kotun tarayya ta Abuja ta aika da mutum 10 da ake zargi da hannu a zanga-zangar tsadar rayuwa zuwa gidan yari.
Mai shari’a Emeka Nwite, ya aika da maza tara gidan gyaran hali na Kuje sannan ya aika da mace É—aya zuwa gidan yarin Suleja.
Mutum goman da aka gurfanar a gaban kotun sun haÉ—a da Michael Adaramoye da Adeyemi Abayomi da Suleiman Yakubu da Opaoluwa Simon da Angel Innocent.
Sauran sun haÉ—a da Buhari Lawal da Mosiu Sadiq da Bashir Bello da Nuradeen Khamis da kuma Abdulsalam Zubairu.
An gabatar da su ne a gaban kotun inda ake tuhumar su da cin amanar ƙasa da yi wa gwamnati bore da kuma yunƙurin hargitsa kasar nan.
Alƙalin ya kuma saka ranar 11 ga watan Satumba a matsayin ranar da zai yanke hukunci dangane da buƙatar bayar da belin waɗanda ake zargin.