Hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA, ta musanta labarin da ke yawo cewa ta bayar da izinin gina shaguna a jikin wata makaranta da ke Zawachiki a karamar hukumar Kumbotso.
Mamba a kwamitin duba gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba na hukumar Sadiq Ali Sango ne ya sanar da hakan yayin ganawa da menama labarai.
Sango ya ce shagunan da ake zargin hukumar ta yanka suna gefen wani fili ne mallakin gwamnatin Kano mai lamba TP/KASEPPA/246, wanda basu da alaka da wata makaranta, kamar yadda wasu ke zargi.
A baya dai wasu sun yi zargin hukumar ta bayar da izinin gina shaguna a jikin wata makaranta a Zawachiki da ke karamar hukumar Kumbotso sai dai hukumar ta musanta labarin.