Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMutanen da suka mutu sanadiyar ambaliyar ruwa a Jigawa sun karu zuwa...

Mutanen da suka mutu sanadiyar ambaliyar ruwa a Jigawa sun karu zuwa talati yayin da gonaki fiye da duba tara suka lalace.

Date:

Mutanen da suka rasu sanadyiyar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa sun karu zuwa talatin, yayin da gonaki fiye da kadada dubu tara suka lalace, tare da rushewar gidaje fiye da dubu hudu.

A iya cewa ambaliyar bana ta bambanta da aka saba gani duk da sanin cewa hukumar kula da yanayi ta kasa tayi hasashen Jigawa na daga cikin jihohin da zasu fuskanci ambaliya a bana.

A yanzu dai fiye da yankunan jihar casa’in ne suka fuskanci ambaliyar, yayin da shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Haruna Mairiga, ya ce gwamnati zata taimakawa wadanda iftila’in ya shafa da buhunan shinkafa da gero da gari da magunguna.

Ya ce suna aiki ba-dare-ba-rana domin tallafawa wadanda abun ya shafa.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...