Daga Ahmad Hamisu Gwale
Hukumar Kwallon Kafa Ta Nahiyar Afrika CAF, ta sanar da jerin kasashe 18 da suka samu tikitin buga gasar kwallon kafa ta CHAN.
Gasar CHAN ta ‘yan wasan da suke buga kwallo a cikin gida a nahiyar Afrika ce, kuma za ta gudana a kasashen Kenya da Tanzania da kuma Uganda daga 1 zuwa 28 ga Fabrairun 2025.
A karshen mako Super Eagle B ta bi sahun kasashen da za su buga gasar ta CHAN bayan doke Ghana da ci 3-1 a ranar Asabar.
Cikin kasashe 18 da suka samu tikitin buga gasar sun hada da Najeriy da Morocco da Nijar da Angola da Madagascar da masu masaukin baki Kenya da Tanzania da kuma Uganda.
Sauran sune Guinea da Senegal da Mauritania da Burkina Faso da Central African Republic da Congo, da Congo, da Sudan da Rwanda kuma Zambia.