Ahmad Hamisu Gwale
Sabon shugabancin hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya sanar da soke kwantaragin Paul Offor a matsayin mai horar da kungiyar ta Sai Masu gida.
A wata sanarwa da sashen yada labarai na hukumar gudanarwar kungiyar ya fitar, yace an soke kwantaragin Paul ne bisa fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.
Shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Ali Nayara Mai Samba, ya godewa Paul Offor bisa gudunmawar da ya bayar wajen ciyar da Kano Pillars gaba.
Kasa da wata guda, tsohon shugaban kungiyar ta Kano Pillars Alhaji Babangida Umar Little ya nada Paul Offor mai horar da Kungiyar, sai dai tuni sabon shugaban kungiyar ya sanar da soke kwantaragin Paul din.
Kano Pillars dai yanzu haka na ci gaba da tunkarar kakar wasannin shekarar 2024/2025 da ake shirin farawa a wata mai kamawa na Augusta.