Ba kamar yadda ake zargin na siyasa bane dake alaka da gwamanati inji shi.
Sakataren kungiyar Izala ta kasa Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa sun shirya gudanar da babban taron mahadata Qur’ani na kasa da kyakkyawar manufa, ba kamar yadda wasu ke zargin cewa akwai siyasa a ciki ba.
Shehun malamin ya bayyana hakan ne yayin wata lakca da aka gudanar a Abuja a makon nan
“Taron ya samu goyon bayan wasu daga cikin manyan malamai wadanda suka hada da Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo da Dakta Bashi Aliyu Umar da Dakta Jalo Jalingo da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Farfesa Mansur Sakkwato da Farfesa Salisu Shehu da Imam Ahmad Ansaruddi da kuma sauran manyan malaman addinin musulunci daga bangarori daban daban” in ji shi.
Ya kuma musanta zargin cewa an tsame sunayen wasu wadanda ba za a gayyace su taron ba.