Asusun tallafa wa Ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka ga mahukuntan ƙasar Somaliya kan hukuncin kisa da aka yanke wa wasu matasa huɗu da ake zargi da alaka da ƙungiyar Al-Shabab.
UNICEF ya ce an kashe mutanen huɗu ne a jihar Puntland mai cin gashin kanta a ƙarshen makon da ya gabata saboda laifukan da suka aikata lokacin da suke ƙasa da shekara 18.
Ta ce kotunan soji ba su da wani tsari na musamman na shari’ar yara don haka bai kamata su riƙa yanke wa yara hukunci ba.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata, an kashe mutum 10 ta hanyar harbin bindiga, saboda samunsu da hannu a kisan gilla da tashin bama-bamai a birnin Gaalkayo.