Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi tsohon Gwamnan, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya ja girman sa, yana mai cewa shirun da yake yi ba tsoro ba ne.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron ƙaddamar da ɗan takarar Sanatan Kano ta Kudu da ya gudana a ƙaramar hukumar Rano, inda ya ce lokaci ya yi da za’a mutunta juna da kaucewa furucin da ka iya haifar da rashin fahimta.
Kalaman Gwamnan na zuwa ne kwana guda bayan da Kwankwaso ya gudanar da wata hira da manema labarai a gidansa da ke Miller.
