Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi sabbin jami’an rundunar da suka kammala karbar horo kan amfani da makamansu cikin ƙwarewa, kiyaye doka da mutunta haƙƙin ɗan Adam.
CP Bakori Ya yi wannan kira ne yayin wani atisayen harbi da aka gudanar a filin Hawan Kalibawa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Ya ce manufar horaswar ita ce ƙara wa jami’an ƙwarewa wajen sarrafa makamai, inganta shirin ko-ta-kwana da kuma tabbatar da cewa suna gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da bin ƙa’idojin aikin ‘yan sanda.
Ya ce rundunar ba za ta lamunci duk wani amfani da makami ba bisa ƙa’ida, yana mai umartar jami’an da su kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kauce wa duk wani aiki da zai tauye haƙƙin al’umma.
