Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa Kwalejin ’yan Sanda ta Wudil, domin ƙarfafa ayyukanta na horas da manyan jami’an ’yan sanda da inganta tsaron ƙasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da sabon Kwamandan kwalejin, Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, AIG Auwal Musa Muhammad, ya kai masa ziyarar gaisuwa a gidan gwamnatin Kano.
A cewar gwamna Abba gwamnatin sa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da fatan cewa ƙwarewar AIG Auwal Musa za ta ƙara inganta ayyukan kwalejin.
Gwamna Abba ya bayyana kwalejin a matsayin muhimmiyar cibiyar horas da jami’an ’yan sanda, yana mai cewa jami’an da kwalejin ke samarwa na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro a faɗin Najeriya.
Da yake jawabi, sabon Kwamandan, AIG Auwal Musa Muhammad, ya ce ya kai ziyarar ne domin gabatar da kansa ga gwamnan tare da yabawa gwamnatin Kano kan kulawar da take baiwa harkokin tsaro.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito AIG Auwal Musa na tabbatar da cewa kwalejin za ta ƙara ƙaimi wajen horas da jami’an ’yan sanda bisa buƙatun tsaron zamani da sauyin yanayin aikin ’yan sanda.
