Majalisar dattawa ta umarci kwamitocinta da su dakatar da duk wani aiki da ya shafi tantance kudurorin kafa sabbin jami’o’i da sauran manyan makarantu a ƙasar.
Matakin na zuwa ne domin aiwatar da umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da kafa sabbin manyan makarantu, da nufin ƙarfafa da inganta waɗanda ake da su a halin yanzu.
Hakan na nufin ba za a ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa kan waɗannan kudurori ba har sai an sake duba wannan mataki.
