Saurari premier Radio
25.3 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiJamhuriyar Nijar ta sanar da cewa ta cigaba da safarar man fetur...

Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa ta cigaba da safarar man fetur ta Jamhuriyar Benin.

Date:

Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa ta cigaba da safarar man fetur ta Jamhuriyar Benin bayan tsaikon da aka samu a sandiyar saɓani da ya shiga tsakanin ƙasashen biyu na kusan wata biyu.

Rediyo Faransa ne ya ruwaito cewa jirgi mai ɗauke da man fetur ɗin, wanda ya bar Sèmè-Podji a jiya shi ne na biyu tun bayan kammala aikin bututun man Nijar zuwa Benin, wanda China ta yi.

Dawo da kasuwancin man fetur ɗin da Nijar ta yi daga tashar da ke cikin Jamhuriyar Benin, ya nuna alamar an samu maslaha bayan Jamhuriyar Benin ta dakatar da harkokin kasuwancin man fetur ɗin na Nijar a watan Mayu saboda Nijar ɗin ta ƙi buɗe bodarta saboda wasu matsalolin diflomasiya.

Nijar ta zargi Benin ta bai wa “Æ´an ta’adda” sansanin samun horo wanda a cewarta Faransa ke É—aukar nauyi, zargin da gwamnatin Patrice Talon ta Æ™aryata.

Alaƙa tsakanin ƙasashen biyu ta yi tsami ne tun bayan da sojoji suka hamɓarar da tsohon Shugaban Ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...