Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi rajistar sababbin masu kada ƙuri’a sama da miliyan 6 a duk faɗin kasar nan yayin gudanar da rajistar masu zaɓe ta dindindin gabanin babban zaɓen 2027.
An samu wannan adadi ne bayan kammala mataki uku na rajistar masu zaɓe, inda aka tsawaita wa’adin rajistar da makonni biyu daga ranar 10 ga Yuli zuwa ranar 26 ga Yuli, 2026.
Sai dai INEC ta bayyana wa jaridar Daily Trust cewa, har yanzu wannan adadi na wucin gadi ne, domin ana ci gaba da tantance bayanan masu rajista kafin fitar da adadi na ƙarshe.
A cewar shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe na hukumar INEC, Muhammad Kudu Haruna, mataki na uku shi ne na ƙarshe a shirin rajistar.
Rahotanni sun nuna cewa, mataki na farko da aka gudanar tsakanin watan Agusta zuwa Disamban 2025 ya samar da sabbin masu rajista sama da miliyan 2
Mataki na biyu kuma ya ƙara mutum sama da miliyan 1 yayin da mataki na uku ya kawo adadin sama da miliyan 2, wanda ya sa jimillar rajistar ta haura sama da miliyan 6.
Hukumar ta ce za ta baje kolin kundin masu zaɓe a watan Agusta domin bai wa jama’a damar gabatar da ƙorafe-ƙorafe ko gyaran bayanai.
