Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 28 ga Nuwamba, 2026, domin gudanar da gwajin zaɓen shugaban ƙasa a faɗin Najeriya, gabanin babban zaɓen 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan yayin wani taro a Chatham House da ke birnin London, inda ya ce gwajin zai taimaka wajen tantance ingancin na’urorin BVAS da tsarin tura sakamakon zaɓe ta intanet.
Ya ce hukumar ta samar da sabbin matakan kariya domin hana shigar da sakamakon ƙuri’a marasa inganci ko waɗanda ke nuna ƙuri’un da suka zarce adadin masu kaɗa ƙuri’a a shafin IReV.
Amupitan ya ƙara da cewa INEC ta fara rarraba wasu kayayyakin zaɓe zuwa jihohi, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen gudanar da babban zaɓen 2027.
