Saurari premier Radio
24 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiNi zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 ...

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

Date:

“Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027” – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP a kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce shi ne zai yi nasarar lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa Kwankwaso na wannan furuci ne a ranar Asabar a lokacin da ya kaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP, a kan titin IBB, a jihar Katsina.

Kwankwaso, wanda shi ne ya yi wa jam’iyyar ta NNPP takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya bayyana kwarin gwiwar yin nasara a zaben da ke tafe.

Sanata Kwankwaso wanda yaje jihar Katsina domin yin ta’aziyyar rasuwar Hajiya Dada mahaifiyar tsohon shugaban Nijeriya Marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...