Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ƙalubalanci ’yan majalisar dokokin jihar da takwarorin su na tarayya da su yi koyi da Sanata Kawu Sumaila wajen wakiltar al’umma da kuma kawo ayyukan ci gaba zuwa mazabunsu.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ƙungiyar muryar kano ta kudu ta shirya taro, tare da gayyatar Sanata Kawu Sumaila, inda ya gabatar mata da rahoton ayyukan da ya gudanar da waɗanda ya taimaka wajen samarwa a yankin.
Gwamnan Abba ya bayyana Kawu Sumaila a matsayin jakadan kwarai ga al’ummar da yake wakilta, yana mai cewa wakilci nagari bai tsaya ga riƙe mukami ba, sai dai ya ƙunshi kusanci da jama’a, fahimtar buƙatunsu da kuma samar da mafita ga matsalolinsu.
A nasa jawabin, Sanata Kawu Sumaila ya yi bayyani mai tsawo kan ayyuka da kudurorin da ya gabatar a majalisar dattawan, tare da bayyana irin ayyukan da ya kawo a kano ta kudu a fannonin tsaro, kiwon lafiya, ilimi da noma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na jinjinawa al’ummar Kano ta Kudu bisa haɗin kansu da kuma ɗaukar matsayar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027, yana mai cewa haɗin kai da haɗin gwiwa na da muhimmanci wajen cimma muradun siyasa da ci gaban Kano.
