Rahotanni daga gabashin Kongo na cewa ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari da ke kusa da kan iyakar Uganda.
Hakan ya faru ne a jiya Asabar, daidai lokacin da wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta wata guda ta zo ƙarshe.
Mazauna garin sun ce dakarun dake goyon bayan gwmanati sun janye daga garin bayan da ƴan tawayen suka shiga garin.
Wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Kongon da Angola ta shirya tare da sa hannun – Congo da Rwanda, za ta fara aiki yau.
Sai dai ƴan tawayen M23 ɗin sun kafe cewa ba su cikin yarjejeniyar da gwamnatin Kongo da ta Rwanda suka sanya wa hannu a ranar Alhamis.