Jam’iyyar PDP ta rushe shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano tare da sauke shugaban jam’iyyar na jihar, Dr Bello Gambo Bichi.
Matakin ya fito ne daga uwar jam’iyyar, inda wata wasiƙa mai kwanan wata 24 ga Satumba 2026 ta bayyana.
A cewar wasiƙar, matakin ya shafi shugabancin jam’iyyar na jihar ne kawai, yayin da kwamitocin jam’iyyar na ƙananan hukumomi da mazabu ba su cikin rushewar.
Jam’iyyar ta kuma umarci Kwamitin Rikon Kwarya na Arewa maso Yamma da ya kula da harkokin PDP a Kano har zuwa lokacin da za a kafa sabon Kwamitin Ayyuka na Jihar.
Da yake magana kan matakin, Bichi ya ce ya amince da rushewar ne a matsayin sadaukarwa domin samar da sulhu da haɗin kai tsakanin ‘yan jam’iyyar, tare da ƙarfafa PDP a jihar.
Ya ce matakin na daga cikin sharuɗɗan sulhun da aka cimma, musamman bayan sauya tsohon ɗan takarar gwamnan PDP, Dalhatu, da Muhammad Abacha a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Bichi ya ce ya amince da sauyin ne saboda burin sake haɗa kan jam’iyyar da kuma ƙara mata ƙarfi gabanin zaɓe.
