Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKNUPDA ta musanta zargin gina shaguna a jikin makarantar Zawachiki

KNUPDA ta musanta zargin gina shaguna a jikin makarantar Zawachiki

Date:

Hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA, ta musanta labarin da ke yawo cewa ta bayar da izinin gina shaguna a jikin wata makaranta da ke Zawachiki a karamar hukumar Kumbotso.

Mamba a kwamitin duba gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba na hukumar Sadiq Ali Sango ne ya sanar da hakan yayin ganawa da menama labarai.

Sango ya ce shagunan da ake zargin hukumar ta yanka suna gefen wani fili ne mallakin gwamnatin Kano mai lamba TP/KASEPPA/246, wanda basu da alaka da wata makaranta, kamar yadda wasu ke zargi.

A baya dai wasu sun yi zargin hukumar ta bayar da izinin gina shaguna a jikin wata makaranta a Zawachiki da ke karamar hukumar Kumbotso sai dai hukumar ta musanta labarin.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...