Hukumar zabe mai zaman ta jihar Kano KANSIEC ta rage lokacin gudanar da zaban kananan hukumomi zuwa ranar 26 ga watan Oktoban 2024, sabanin ranar 30 ga watan Nuwamba da ta sanya a baya.
Shugaban hukumar, Ferfasa Sani Lawan Malunfashi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudunar yau Juma’a.
Ya ce sun rage lokacin gudanar da zaban ne domin biyayya ga hukuncin da kotun koli ta yi na bai wa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu.
Ferfasa Lawan Malunfashi ya kara da cewa, dukkanin harkoki siyasa za a fara gabatar da su ne daga ranar 1 ga watan Satumba mai kama wa zuwa daren 25 ga watan Oktoba.