Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tace kudaden...

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tace kudaden da ake zargin anyi badakalar su a harkar magani ba su haura miliyan 500.

Date:

Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, tace zata gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a badakalar bada kwangilar sayen magani da kudin da aka karba daga hannun kananan hukumomin jihar nan a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan lokacin da yake wata zantawa da Premier Radio a yau talata.

Muhyi yace ya zuwa yanzu binciken farko da hukumar su ta fara gudanarwa ya tabbatar da cewar tabbas an umarci kananan hukumomi 44 na jihar da su bayar da kudaden tare da bada kwangilar duk kuwa da cewar anyi hakan ne ba tare da sani Gwamna Abba Kabir Yusif ba.

Sai dai Muhyi yace yawan kudaden da aka karba a hannu kananan hukumomin bai kai yawan da ake ta yayatawa a kafafen yada labarai ba, inda yace adadin kudin gaba daya bai wuce naira miliyan dari 3 ba.

A cewarsa, hukumar ta su kuma tana binciken zargin karkatar da kayan abinci da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Abba Yusuf, Shehu Sagagi ya yi.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...