Saurari premier Radio
25.3 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar yaki da cin hanci da rashawa a nan Kano ta kama...

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a nan Kano ta kama dan uwan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a karkatar da kudin kwangilar magunguna.

Date:

Hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama wasu mutane 5, wadanda suka hadar da Alhaji Muhammed Kabara babban sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi da kula da harkokin masarautu, biyo bayan zarginsu da sama da fadi da wasu makudan kudade da sunan kwangilar magunguna.

Mai magana da yawun hukumar Kabiru Kabiru ya tabbatarwa da manema labarai kama mutanen, yana mai cewa a binciken da suka fara sun gano cewa kananan hukumomi 44 na ware wasu kudade da suna kwangilar magani kuma kudin na fita amma babu maganin a kasa.

Daga cikin mutanen da hukumar ta kama akwai shugaban karamar hukumar Tarauni Alhaji Abdullahi Bashir, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar shugabannin kanannan hukumomi ta kasa reshen nan Kano, sai kuma shugaban kamfanin magunguna na Novomed Garba Kwankwaso, dan’uwan madugun darikar kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, biyo bayan yadda zargin ya karkata kansa a badakalar.

Wadanda aka kama din anan zarginsu da sama da fadi da makudan kudade wadanda ake zargin sun taskace su da sunan baiwa kamfanin na NOVOMED kwangilar magunguna raba magunguna ga kananan hukumomi 38, duk kuwa da cewa hakan ya sabawa dokokin gudanar da ayyukan gwamnati.

Mai magana da yawun hukumar ya kara da cewa wadanda suka kama din yanzu haka suna tsare a maajiyar hukumar, ya yin da hukumar ta ci gaba da gudanar da bincike kan badakalar.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...