Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC reshen jihar Kano ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya da ke Kano, wanda ya hana jami’anta gudanar da aiki a hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi, tare da takaita aikinsu zuwa manyan hanyoyin gwamnatin tarayya kaɗai.
Mai shari’a M. S. Shuaibu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, bayan ƙarar da wani lauya a Kano, Barrista Abba Hikima, ya shigar.
Barrista Hikima ya kai ƙarar ne bayan ya zargi jami’an FRSC da kafa shingayen bincike a kan titunan cikin birnin Kano tun a watan Yulin shekarar 2025, inda ake tsayar da direbobi ba tare da sun aikata wani laifin hanya ba.
A hukuncinsa, Mai shari’a Shuaibu ya ce jami’an FRSC sun wuce iyakar ikon da doka ta ba su ta hanyar gudanar da aiki a hanyoyin jiha.
Ya ce hakan ya saɓa wa haƙƙin yan ƙasa na samun yancin walwala da zirga-zirga kamar yadda sashe na 35 da na 41 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya tanada.
Kotun ta amince da dukkan buƙatun da Barrista Hikima ya gabatar, ciki har da umarnin haramta wa FRSC aiki a hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi a Kano, umarnin ta wallafa ba da haƙuri a wata jaridar ƙasa, da kuma biyan diyyar Naira dubu 800.
Sai dai da take mayar da martani, FRSC ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Kano, CRC Abdullahi Aliyu Labaran, ta ce tana mutunta hukuncin kotu, amma ana fassara shi ba daidai ba a kafafen sada zumunta.
Hukumar ta jaddada cewa hukuncin bai soke ikon da Dokar Kafa FRSC ta shekarar 2007 ta ba ta ba, illa dai ya takaita aikinta a Kano zuwa manyan hanyoyin gwamnatin tarayya.
Ta bayyana cewa hanyoyin da za ta ci gaba da aiki a kansu sun haɗa da Kano–Zariya, Kano–Katsina, Kano–Maiduguri, Kano Western Bypass, Airport Road da Murtala Mohammed Way.
FRSC ta kuma nuna damuwa kan saƙonnin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da ke ƙarfafa direbobi su ƙi bin umarnin jami’anta, tana mai cewa hakan na iya haddasa rikici tare da barazana ga zaman lafiya.
Hukumar ta ce tana ganin ba a yi cikakken la’akari da hujjojinta ba yayin shari’ar, saboda haka ta yanke shawarar ɗaukaka ƙara.
