Hambararren Shugaban kasar Siriya, Bashar al-Assad, da iyalinsa sun isa Moscow bayan zarge-zargen mutuwarsa a hadarin jirgi a kokarinsa na tserewa daga kasar
Wasu majiyoyi daga fadar Kremlin sun ce an ba Assad da iyalinsa mafaka a Rasha.
Tun bayan faduwar gwamnatin Assad a ranar Lahadi, aka tabbatar da ya bar kasar ba kuma san inda ya dosa ba.
Hayat Tahrir al-Sham (HTS) wata ƙungiya mai rajin addinin Islama ce ta yi nasarar ƙaddamar da hari mai muni a arewa maso yammacin ƙasar a Larabar makon jiya, bayan ta yi haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyin ‘yan tawaye
Kungiyar ta HTS ta samu nasarar kwace wasu manyan biranen kasar da hakan ta kai ga kwace Damascus a ranar Lahadi.
Karshen mulkin sama da shekara 50
Zuri’ar Assad ta yi mulkin kama karya na tsawon shekara 53 a Syria.
Shugaba Bashar al-Assad ya karɓi ragamar mulkin kasar ne a shekara ta 2000, bayan mahaifinsa ya yi mulkin aƙalla shekara 30.
Shekara 13 da suka wuce ya yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe masu zanga-zangar lumana, lamarin da ya sauya zuwa yaƙin basasa da ya ɗaiɗaita ƙasar.
Tsawon wannan lokaci shugaba Assad na samun goyon bayan Irin da kuma Rasha a mulkin da ake hasashe kashe mutane fiye da rabin miliyan da tilasta wa wasu miliyan 12 barin muhallansu.
An ga mutane na ta murna da sowa a babban birnin da jin labarin tserewar Assad da kuma kawo karshen gwamnatinsa ta kama-karya a cewar rahotanni.
Shiga halin dar-dar a Gabas Ta Tsakiya
BBC ta rawaito cewa, shugabannin kasashe daban-daban a yankin Gabas ta Tsakiya na bayyana matsayi da ra’ayoyinsu game da faduwar gwamnatin Bashar Al- Assad.
Yayin da wasu ke maraba da faduwar dadaddiyar gwamnatin ta Assad, tare da bayyana kwarin gwiwa na samar da makoma mai kyau ga kasar wasu kuwa na nuna fargaba da dari-dari ne.
A Iran ministan harkokin waje, Abbas Araghchi, wanda ya gaya wa kafofin yada labarai na kasar cewa Iran ka iya zama kawa ce ta Syria, to a mma tana gefe tana ganin abubuwan da ke faruwa.
Araghchi, ya ce ya yi mamakin yadda sojojin Syria suka kasa dakatar da ‘yan tawayen. ia a