Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta zargin cewa yana yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu aiki a boye domin taimaka masa wajen yin nasara a zaben 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Global TV, inda ya ce mutane marasa hankali ne kawai za su yarda da irin wannan zargi.
Ya ce shi da magoya bayansa suna aiki ne kawai domin jam’iyyar NDC, ba domin wata jam’iyya ko dan takara ba.
Ya kara da cewa duk da cewa Tinubu babban abokinsa ne tun shekaru da dama, hakan ba yana nufin za su hada akidunsu na siyasa ba.
Kwankwaso ya kuma zargi makusantan shugaban kasa da boye masa hakikanin matsalolin da kasar ke fuskanta, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun fi mayar da hankali wajen jan Gwamnoni zuwa APC.
Game da hadakarsa da Peter Obi a jam’iyyar NDC, Kwankwaso ya ce sun zabi goyon bayan Obi ne bayan nazari da suka yi, inda suka ga shi ne mafi dacewa daga yankin kudancin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa hadakar tasu na da isasshen lokaci kafin zaben 2027 domin jawo hankalin ‘yan Najeriya da kuma bayyana gaskiya kan rade-radin da ake yadawa.
