Majalisar magabata ta kasa, ta zargi masu zanga-zangar matsin rayuwa da yunkurin sauya gwamnati a kwanakin baya, wanda hakan ya sa ta kada kuri’ar amincewa ga Bola Ahmad Tinubu a matsayinsa na shugaban kasa, tare da nuna rashin kin yarda da duk wani yunƙurin sauyin gwamnati ba ta hanyar zabe ba.
Yayin zaman majalisar wanda ya gudana Jiya Talata a fadar shugaban kasa, ta kuma tattauna kan matsalolin da suka shafi tsaro a faɗin ƙasar nan, da batun tattalin arziki, da kuma halin yunwa da ake ci gaba da kokawa akai.