Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumar Kwastam ta bari a fara shigowa da abincin da aka cire wa haraji a cikin kasar nan batare da Wani Bata Lokaci ba.
Idan za a tuna dai a watan Yuni da ya gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci a cire harajin shigo da shinkafa, masara, gero, wake da sauran su na tsawon wata 6 domin rage wa yan kasa tsadar rayuwa.
Ana Kallon Matakin Zai Taimaka Wajen Saukaka Tsadar Kayan Masarufi da al’umma ke Amfani Dashi yau da Gobe
Rahotanni dai sun nuna Al’ummar Ƙasar nan na Cigaba da kokawa akan Halin Matsin rayuwa da kuma hauhawar Farashin Kayan Amfanin yau da Kullum musamman Abinci
Masana na Kallon Matakin bayar da damar Shigo da Abinci Daga Kasashen Ketare Zai Taimaka Wajen karyar da Farashin Kayan Masarufi Dake nan gida Nigeria.