Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin haɗin gwiwa tsakanin ts da makarantun gaba da sakandaren jihar, domin faɗaɗa shirin dasa bishiyoyi domin kare muhalli a faɗin jihar.
Kwamishinan albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi na Kano, Dr Dahiru Muhammad Hashim, ne ya jagoranci shirin a Kwalejin LEGAL.
Dr Dahiru ya ce shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na faɗaɗa dashen bishiyoyi, wanda a bana ake sa ran za’a dasa bishiyoyi miliyan 1, inda ya ce
dasa bishiyoyin na da muhimmanci wajen tsaftace iska, rage zafin yanayi, yaƙi da zaizayar ƙasa da kuma kare muhalli.
A nasa ɓangaren, muƙaddashin shugaban kwalejin Dr Tamasi Ali Mu’az 6a buƙaci gwamnatin Kano da ta taimaka wajen samar da ingantaccen ruwan sha, da gina ɗakin noman zamani a kwalejin domin bunƙasa koyar da aikin gona da bincike.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishinan na tabbatar da aniyar gwamnati na tallafawa makarantu da magance matsalolin muhalli da samar da ruwa, inda ya ce za’a ci gaba da inganta tsarin samar da ruwa a Kano, tare da bada umarnin a haƙawa kwalejin rijiyar burtsatse domin samar mata da ruwa cikin gaggawa.
