Gwamnatin Kano ta ce ta farfado da tashar samar da ruwan sha ta Tudun Wada bayan shafe shekaru bata aiki, inda yanzu take samar da lita miliyan 2.2 na ruwan famfo a kullum.
Kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa ta Kano, Dr Dahiru Hashim, ne ya bayyana hakan yayin duba yadda tashar ke aiki.
Dr Hashim ya ce farfaɗo da tashar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba ya dawo da ruwan famfo a unguwannin Gawo, Tsauni, Tsohuwar Nitel da Unguwar Gabas.
Kwamshinan ya ce ma’aikatar na ci gaba da gyaran bututun ruwa da wuraren da ke zubar da ruwa a sassa daban-daban na yankunan, domin inganta rabon ruwa da tabbatar da isar da shi ga al’umma ba tare da asara mai yawa ba.
Kwamishinan ya kuma bayyana shirin ma’aikatar na ƙara ƙarfin tashar daga lita miliyan 2.2 zuwa miliyan 4.5 a kullum, matakin da zai faɗaɗa samar da ruwa zuwa wasu al’ummomi da ƙauyuka a faɗin ƙaramar hukumar Tudun Wada.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Dahiru na tabbatarwa mazauna yankin cewa ma’aikatar za ta ci gaba da sanya ido sosai domin tabbatar da dorewar aikin tashar da ingantaccen samar da ruwan sha ga al’umma.
