Gwamntin jihar Kebbi ta bai wa ma’aikatan kiwon lafiya na wucin gadi su fiye da 200 takardun kama aiki na dindindin bayan wani korafi da suka yi a lokacin gabatar da shirin ‘A Faɗa A Cika’ na BBC Hausa da haɗin gwiwar Gidauniyar MacArthur.
Haka ma gwamnatin ta bayyana cewa ta cika alkawarin sama wa manoman shinkafa da suka yi korafi fanfunan ban ruwa har kimanin 6,000.
Gwamnan jihar Dakta Nasir Kauran Gwandu da ya ke amsa tambaya a lokacin shirin da ya gudana a jihar Kebbi ya ce tattaunawar da aka yi ta haifar da alfanu.
Ba iya jihar Kebbi ba, kusan a jihohin wannan kasa akwai ma’aikatan lafiya na wucin gadi da dama dake ci gaba da aikin taimakon marasa lafiya, duk kuwa da yadda ake fama da karancin likitoci a wannan kasa, lamarin da ya sanya wasu gwamnonin kan mayar da hankali wajen tabbatar da takardar daukar aiki ga ma;aikatan wucin gadin a lokaci zuwa lokaci.