Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Ghana ta kaddamar da wata babbar cibiyar sarrafa albarkatun mai da...

Gwamnatin Ghana ta kaddamar da wata babbar cibiyar sarrafa albarkatun mai da za ta ba kasar damar mallakar fetur mafi girma a nahiyar Africa.

Date:

Gwamnatin Ghana ta kaddamar da wata babbar cibiyar sarrafa albarkatun mai da za ta ba kasar damar mallakar matatar fetur mafi girma a nahiyar Afrika.

Ana sanya ran matatar da za ta kasance karkashin wannan cibiya zata rika tace danyen man fetur akalla ganga dubu dari tara kowacce rana, matakin da idan ya tabbata zai sanya Ghana gaban kowacce kasa a nahiyar Afrika ta fannin tace mai mafi yawa.

Hukumar kula da harkokin man fetur a kasar, ta ce ana sa ran nan da shekaru biyar za a samar da matatu uku wadanda duka zasu rika aiki kamar yadda ya kamata.

Kididdiga ta nuna cewa, matukar aka cimma wannan buri, gwamnati za ta samu karin kashi saba’in cikin dari na yawan kasafin kudin da ake bukata, da kuma samar da guraben ayyuka sama da dubu dari takwas.

Wannan dai wani gagarumin ci gaba ne da wannan kasa ta Ghana ta samu, wadda ta dogara da shigar da tattaccen man fetur daga ketare, yadda kuma zai saukakawa al’ummarta ta hanyoyi da dama.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...