Saurari premier Radio
24 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnati za ta sauyawa makarantar sakandiren Maikwatashi muhalli zuwa Kaura Goje

Gwamnati za ta sauyawa makarantar sakandiren Maikwatashi muhalli zuwa Kaura Goje

Date:

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dauke makarantar maikwatashi daga muhallin da take unguwar Sabon Gari zuwa Kaura Goje biyo bayan lalacewar da makarantar tayi tare da zamowa mafakar bata gari.

Da yake gabatar da kudurin, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa a zauren majalisar dokokin Injiniya Yusif Bello Aliyu yace kasancewar makarantar ta maikwatashi tana da tsohon tarihi a fannin ilimin jihar nan.

Ya ce yanzu haka makarantar ta zama mafakar ‘yan daba, barayi da ‘yan shaye-shaye wadanda ke barazaba ga jama’a.

A dai zaman na yau litinin majalisar ta amince da kudurin da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kiru Usman Abubakar Tasi’u Kiru ya gabatar mata na a gina hanyar ruwa domin al’ummar dake karamar hukumarsa.

Ya ce hakan zai taimakawa noman rani da sauran bukatu.

Wakilinmu na majalisar dokokin, Kamal Umar Kurna, ya rawaito cewa dan majalisar na Kiru ya na cewa babbar matasalar da matasan yankin suke fuskanta sanadiyyar tafiyar matasan su ya zuwa kudancin kasar nan sun hada da koyo munanan dabi’u da yawaitar samun hadura a hanya wanda yake ajalin matasan su.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...