Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin sabbin masu BA shi shawara na musamman tare da sauyawa wasu daga cikin masu rike da mukaman ayyuka, a wani yunkuri na kara inganta tafiyar da gwamnati da kyautata ayyukan yiwa al’umma hidima.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar, gwamnan ya soke mukaman mai bashi shawara kan harkokin cikin Gida da kuma Mai bashu shawara kan ofishin gwamnatin na Abuja, inda aka mayar da wadanda ke rike da mukaman zuwa wasu sabbin ayyuka.
Daga sauye-sauyen da aka yi, Habiba Mustapha Barwa ta koma Mai bada Shawara kan ayyuka na Musamman na Mata, yayin da Umar Uba Akawu ya zama Mai bada Shawara a ofishin Majalisar Zartarwa kan Harkokin Siyasa.
Haka kuma an sauyawa Akibu Isa Murtala aiki zuwa harkokin kula da ma’aikata, Ibrahim Adam zuwa harkokin sada zumunta na zamani, yayin da Nasiru Isa Dikko ya koma bangaren tallafawa da bunkasa rayuwar al’umma.
Gwamnan ya kuma amince da nadin Bello Nuhu Bello a matsayin Mai bada Shawara kan Mulki a ofishin Gwamna, Ahmed Muhammad Aruwa a matsayin Mai bada Shawara kan yada Labarai, Buhari Sule Kura kan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu, da Yahuza Ado ‘Yankaba a matsayin Mai bada Shawara kan Tashoshin Mota.
Sauran sabbin wadanda aka nada sun hada da Ahmed Tijjani Musa, Ibrahim Hamisu Rimi, Mustapha Abdullahi Rabiu Kura, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama, Naziru Abdullahi Karaye da Tahir Ado Rabi’u u.
Gwamna Yusuf ya ce sauyin na da nufin kara inganta gudanarwar gwamnati da kuma daidaita ayyukan hukumomi da manufofin gwamnatinsa, inda ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su yi aiki da gaskiya, kwarewa da jajircewa domin ci gaban jihar Kano da walwalar al’ummarta.
