Saurari premier Radio
29 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan Kano ya ware biliyan 2 da rabi don inganta noman rani...

Gwamnan Kano ya ware biliyan 2 da rabi don inganta noman rani a karamar hukumar Garko

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

Gwamnatin Kano ta ware naira biliyan 2 da rabi don gyara madatsar ruwa ta kafinciri domin inganta noman rani a karamar hukumar Garko.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin ziyarar duba aikin Titi a karamar hukumar yau Lahadi.

Gwamnan Kanon ya ce an ware kudin ne domin gyara madatsar da fitar da hanyoyin ruwa domin manoman rani.

Dangane da aikin Titin na (Five Kilometer) Abba Kabir Yusuf ya ce ya kwace kwangilar gina shi inda za a baiwa sabon Dan kwangila domin kammalawa cikin kankanin lokaci.

Haka zalika yayi alkawarin daga linkafar Asibitin Karamar hukumar ta Garko zuwa babban Asibitin kwana.

A wani labarin kuma gwamnatin ta ce zata daga Asibitin Karamar Albasu zuwa babban Asibiti domin inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin ziyarar duba aikin Titi mai tagwaye biyu na (five kilomita) da ya kai Karamar hukumar Albasu a Lahadin nan.

Ya ce gwamnatinsa zata samar da karin ma’aikata da daga likkafar Asibitin nan bada jimawa ba.

Gwamnan na Kano ya Kuma duba aikin gyara makarantar ‘yan mata ta kwana dake karamar hukumar wacce aka rufe ta tun zamanin gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Abba Kabir Yusuf ya ce tuni aiki yayi nisa wajen gyara makarantar tare da zuba kayan aiki da malamai domin cigaba da koyar da dalibai.

Ya ce makaranta ce mai tsohon tarihi wacce ta yaye manyan dalibai amma haka kawai tsohuwar gwamnatin data gabata ta rufe ta.

Yayin ziyarar gwamna Abba Kabir Yusuf ya duba matsalar zaizayar kasa a garin Hamdullahi inda yayi alkawarin daukar matakin kawo karshen ta.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...