Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba shanu, raguna, iri, da kayan aikin lambu na zamani ga matasa 340 da suka kammala karatu a cibiyar kiwon dabbobi da tsirrai.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce kowanne daga cikin su zai samu bijiman shanu biyu ko raguna biyu, tare da abincin dabbobin na watanni uku.
Ya ce wannan shiri wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na rage talauci da kuma samarwa matasa sana’o’in dogaro da kai a jihar Kano.
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya jaddada cewa shirin na nuni ne da yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta rayuwar matasa da samar da abinci, wadanda ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban jihar Kano.
Wannan ne kashi na farko na dalibai 340 da aka yaye da suka samu hora a cibiyar kiwon dabbobi da tsirrai da ke Bagauda a karamar hukumar Bebeji, biyo bayan sake bude cibiyar da gwamnatin sa tayi.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, an kuma yi wa wasu matasa 340 rajista a karo na biyu.
Wakilin mu Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf, ya baiwa matasan da suka kammala samun horon kayan aiki da jarin naira dubu 100.
