
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar ilimin bai daya SUBEB ta ja hankalin malaman makaranta da basa zuwa aiki ko suke makara da su kuka da kansu.
Shugaban hukumar Yusuf Kabir ne ya bayyana haka yayin ziyarar da yakai makarantar firamare ta Ado Yola dake a karamar hukumar Kumbotso ranar Laraba.
Yusuf Kabir, ya yabawa malaman makaranta bisa yadda suke jajircewa wajen fitowa aiki tare da koyar da dalibai kamar yadda aka tsara.
Bisa wannan tsarin daukacin Daraktoci Hukumar zasu Kai makamanciyar wannan ziyara a sauran Makarantu da ke yankin.
Ya ce bisa wannan dalilin a yanzu daukacin daraktocin hukumar zasu rinka kai ziyara sauran makarantun dake karkashin hukumar don tabbatar da yanayin koyo da koyarwa mai inganci.
Shugaban hukumar ta SUBEB Yusuf Kabir ya kuma ce gwamnatin jihar Kano, karkashin jagoranci Alhaji Abba Kabir Yusuf tana baiwa ilimi fifikon gaske, ta fuskar samar da kayan koyo da koyarwa da gyara ajujuwan da suka lalace tare da samar da sabbin ajujuwa don rage cinkoson yara da raba kayan sawa na makaranta ga yara ‘yan aji daya duk da nufin samar da ingantaccen ilimi a wannan jiha.
A cewar sa a don haka ne ma suke bi lungu da sako na makarantun jihar nan don tabbatar da cewa Malamai na gudanar da aikin su yadda ya dace.
