Saurari premier Radio
33.3 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan Kano ya bai wa yan kwangila wa'adin kwana 7 su koma...

Gwamnan Kano ya bai wa yan kwangila wa’adin kwana 7 su koma bakin aiki ko ya kwace ayyukan da ya basu

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta bai wa yan kwangila wa’adin kwana 7 su koma bakin aiki ko ta kwace ayyukan daga gurin su.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin duba yadda aikin titi na Five Kilometer ke tafiya a karamar hukumar Ghari a Juma’ar nan.

Ya ce sun bai wa yan kwangila a kowace karamar hukuma umarnin ci gaba da aikin titunan na Five Kilometers ko a sauya su.

Ya ce a wasu kananan hukumomin ma sun karbe daga hannun yan kwangilar da suka gaza kammala aikin inda suka sauya su kuma tuni sabbin yan kwangilar suka kammala aikin.

Gwamna Abba ya bayyana takaicin sa kan yadda gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da aikin titin wanda aka fara a zamanin gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya kuma bude wani Titi a garin Yan Dadi tare da duba yadda ake gudanar da aikace-aikace a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami’a a karamar hukumar ta Ghari.

Ya ce a baya an rufe makarantar amma a yanzu sun sake bude ta domin al’ummar karamar hukumar Ghari su samu damar cigaba da karatu.

Da yake jawabi kantoman karamar hukumar Ghari Sagir Lawan, ya nuna godiyarsa bisa yadda gwamnan Kano ke aiwatar da ayyukan ci gaba a karamar hukumar da jihar Kano baki daya.

Wakilinmu na fadar gwamnati, Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma ce akwai karin ayyuka da titiuna daban daban da za ta aiwatar a karamar hukumar ta Ghari.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...